Header Ads Widget

Kalaman Soyayya Masu Dadi 2023

 KE CE A ZAHIRI KUMA KE CE A CIKIN BACCINA

Kalaman Soyayya Masu Dadi


A kullum na kan kwanta da tinaninki, na kuma farka a cikin mafarkina, na gan ki zaune kusa dani, a cikin wani lambu ma'abocin tsintsaye da furanni. Tabbas a lokacin murmushinki yafi komai jan hankalina, muryarki kuma ke samar da nutsuwata. Ki Huta Lafiya.


KO KIN SAN HAKAN NA FARUWA A KANSA SABODAKE?


Duk inda ya tafi, ko me yake yi yana tinaninki. Ko bacci yake yi ko a farke yake, yana hasaso murmushinki. A dukkan lokacin da kika yi nesa da shi, wajen ganin fuskarki ba ya buƙatar hotonki. Karda ki yi tinanin wani ne na daban face ni. Ina Matuƙar son Ki kamar yadda kika daɗe da sanin hakan.

Kalaman soyayya masu sanyaya Zuciyar Masoya

KALMOMI UKU “INA SON KI”, 

Kalmomi uku na yin sanadin karuwar bugun da zuciyata ke yi, kalmomi uku na sanya kafata karkarwa, kalmomi uku na sanya kaina ya yi ta faman rangaji, bari dai na furta su yau a gare ki ko na huta da azalzalar da zuciyata take yi mini a dangane da hakan, kalmomi uku: INASON KI!!! 


   KECE ABAR TINANINA.

Damuwa? A’a sam, tayaya zan kasance cikin damuwa bayan ako yaushe ke ce abar tinani na? Da ke nake kwana sannan kuma da ke nake tashi a cikin zuciyata. Ina kaunar ki!!

FATAN ZAN SAMU ABUN DA NAKE NEMA?

A koda yaushe ina fatan nasara ta kasance a tare da ke, na kasance mai yin fatan kasancewar farin ciki a cikin zuciyar ki a safiya ko rana, amma shin zaki iya tinawa da wani abu wanda zuciyata ke muradin samu daga gare ki? Ba komai bane face ki mallaka min zuciyar ki ta hanyar sanya ni a cikinta ni kadai ba tare da kin hada ni da kowa ba. 

Zamu Kawo Muku Wadannan Kalaman

  • alamun budurwa na son saurayi
  • kalaman soyayya masu dadi 2022
  • kalaman soyayya masu nishadantarwa
  • kalaman soyayya masu dadi

FUREN SOYAYYA.

Idan har ya kasance zan ke samun kyautar furanni a dukkan lokacin da na hadu da ke, to kuwa ni zan kasance mai ziyartar dausayi ma’abocin firanni masu kamshi na mallaka dukkan lokacina na wannan rana domin girmamaki. Ina son ki sosai a cikin zuciyata.

Post a Comment

0 Comments