Header Ads Widget

Kalaman Soyayya Masu Ratsa Zuciyar Masoya 2023

 KULAWA A SOYAYYA

Hakika Kulawa Itace Mabudin Soyayya domin Itace Take Bayyana Tsantsar Cewa Soyayya Tana Tafiya Daidai.



Wasu Lokuta Masoya da Zarar Sun Fara Gina Soyayya, Bayan Sun Amincewa Juna Akan Zasuyi Soyayya kuma Zasu Farantawa juna ta hanyar nunawa Juna So na gaskiya, Sai Soyayyar Ta Fara Zurfi Sai Rashin Kulawa Ya Fara Yin Tasiri a Tsakaninsu.

Wannan Ya kan Samo Asaline daga Matsalar Jagororin Soyayyar Wadanda Suka Dauki Alwashin Son Juna da Gaskiya.

Ita dai Kulawa Itace Ginshikin Kowane Nau'in Farin Ciki da Shakuwa da Juna Acikin Soyayya, Dan Haka Duk Soyayyar da take Samun Karancin Kulawa Itace Take Rushewa Lokaci daya.

Ga Budurwa Ko Saurayi Ya Cancanta Kulawa da Juna Ta hanyar Musayar Sautin Murya cikin Tsarin Amo da Kalaman da Zasu jefa Zuciya Cikin Nishadi.

Haka Zalika ta hanyar  Kulawa Masoya Suke Rarrashin juna tare da Tausasa Lapazi cikin Sanyin Murya Yayinda Wani Bakon Al'amari na Bakin Ciki Ya riskesu.

Kalaman soyayya masu sanyaya Zuciyar Masoya

Saboda Haka a Shawarce Zanso Masoya Su Kasance Ma'abota Mayar da Hankulansu gami da Tunaninsu Akan Yin Soyayya da Kulawa, Domin Itace Tsantsar Soyayya.

*Dumin Samun Kalamai Masu Dade Wanda Saurayi Zaiyi Ma Yarinyanshi Ko Buduruwa Zatama Saurayinta Ko Mata Zata Ma Mijinta Ko Miji Zaiyi Ma Matanshi 

MU KOYI SOYAYYA DOMIN JIDADIN MU 


Daga cikin irin kalmomin da zaka dinga ji daga wajen wadanda aka karyawa zuciya a soyayya sun hada da:


 


 Na daina soyayya

 So ko wahala

 Bazan sake yin soyayya ba

 Soyayya ko bata lokaci?



Mata suce:

 Maza mayaudara ne

 Najimi ba dan goyo bane

 Namiji kanin ajali

 Duk wacce ta riki namiji Uba zata mutu maraya.

Maza suce :

✎ Mata mayaudara

✎ Mata basu da alqawari

✎ Mata basu gaskiya.

Da sauransu.


Ai ina tunanin rashin fahimtar abinne yake jawo haka ! Idan ka zama mai fushi akan komai to mai zai hana idan aka bata maka rai akan abinci kace ka daina ci ?

 Ko akan kudi kace ka daina kashesu ? Ko idan mutane suka bata maka rai kace ka daina magana da kowa ? In kuma ba zakayi haka ba to me yasa ita soyayya zaka yi mata haka ?!

Ba tare da bata lokaci ba zanyi iya kokarina wajen bayar da haquri ga wadanda aka karyawa zuciya a soyayya tare da nuna musu ko dai kuskuren da suka yi a soyayyar ko kuma akasin da aka samu har hakan ta faru dasu,

 sannan in nuna mana mafita ko abinda ya kamata mutum yayi dan gujewa irin wannan matsalar a nan gaba.

Natsuwar zuciyatah

♥♥♥♥♥♥♥


Natsuwa ke Kara kamani a duk lokacinda nake tunaninki shauki da annashuwa ke kara mamaye zuciyata

♥♥♥♥♥♥♥


Ke kyakkyawace hakan yasa kyawo yake murnar kasancewar sa atare dake, kinada hankalai yakan ke kara saka ni nishadi

♥♥♥♥♥♥♥


Ki tawo gare ni yar gata kece wadda zanyi gata wadda babu karanci domin kullum burina bai wuce na tunanin yadda zan cireki a kunci ba

♥♥♥♥♥♥♥


Sone sanadi kuma silar chanzawar rayuwata taga barin tunanin rayuwa marar tabbaci zuwa ga sabuwar rayuwa mai cike da farin ciki

♥♥♥♥♥♥♥


Tunanin da burina basu taba chanzawa akan zancen tunanin samunki a matsayin matata ina kaunarki gimbiyata

♥♥♥♥♥♥♥

Post a Comment

0 Comments