Header Ads Widget

KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA Na 2023/2024

 KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA Na 2023/2024



GA MASOYA Idan kana tare da budurwa masoyiyar ka, ya kasance kanayi mata kalamai masu dadi na jan hankali, wadanda zasu dinga faranta mata rai.


💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏💏

 

KAMAR HAKA

Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina Kinfita daban a cikin mata.

duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar wace sai ke Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata sai ke kadai Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a gareni.

Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan ta6a mantawa dake ba masoyiyata Nakan raba dare ina mai roqon Allah don neman biyan buqata,


kKamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina.


KALAMAN SOYAYYA

Ina ma a ce na kasance da ke a duk bugun numfashina, kaunarki ce take kara tasiri a ruhina, babban burina na ga bayyanar fitar murmushinki a kan wannan kyakykyawar fuskarki, ya kuma zamana ni ne sanadin hakan. Bana son Allah ya kawo lokacin da za ki fushi da ni sosai kaina ba zai dauka ba, hakika Allah ya wadata ki da abin da mata da yawa suke nema sun rasa ke kanki kin san a cikin jinsinku, mata irinku kadan ne da a ce na iya rubuta labari da a kan fuskarki zan rubuta littafi mai suna kyauta daga Allah, kuma na san zan samu bayanan rubutu kamar guda uku 1,2 da  

Sararin samaniya na cike da taurari, teku na cike da ruwa, doran kasa na cike da ciyayi, amma ni zuciyata cike take da soyayyarki ba ta gushewa kamar yadda taurari ba sa gushewa a sararin samaniya, ba ta kafe wa kamar yadda teku ba ta kafe wa, haka zalika ba ta bushe wa kamar yadda ciyayi ba kamar sukan bushe, soyayyarki dauwamammiya ce a farfajiyar madinan zuciyata da akwai wanda zai tsaga jikina da ya ga jininki yana gudana, a kan k

Post a Comment

0 Comments