Header Ads Widget

Sababbin kalaman Soyayya na 2023

 SO KO YAUDARA KO KADDARA ???

     


 A Yadda Ta Nuna Min Banyi Tunanin Ko Aure Tayi Ba Zata Rabu Dani Ba, Sai Gashi Ta Rabu Dani Ko Tsayayyen Saurayi Babu Balle Kuma Aure. Tace Dani Mubarak Muyi Hakuri Da Junanmu Kawai, Nace Ko Meyasa?

       Tace Saboda Tana Ganin Kamar Aure Tsakaninmu Bamai Yiwuwa Bane, Nace Hmm Kodai Kin Kasa Cimma Manufarki Na Kulla Soyayya Dani Ko Kuma Kin Riga Da Kin Cimma Manufarki???

      Tace Hmmmm. Nace Mexan Kira Hakan Dashi. So Ko Yaudara Ko Kaddara? Tace Kaddara, Nace A'a Yaudara Dai

SOYAYYA SOYAYYACE

Fasihai da masana soyayya sunyi fashin baki akan cewa shin akwai wata soyayyar gaskiya data karya? 

Inda suka tabbata da cewa soyayya soyayyace, Bbu Wata soyayya ta Gaskiya dana karya, ya danganci da yadda kakeji a ranka da kuma yadda ka dauka a zuciyarka 

Wani Lokacin zaka fada soyayyar tare da niyyar cimma wata manufa taka ta yaudara ko karya, amma a gaba bayan ka samu soyayyar sai Kaji cewa da matsala idan ka rabu da wannan soyayya. 

Hakama wani lokaci zaka fada soyayya da tsakakkiyar zuciya, daga bisani ka tsinci kanka Cikin soyayyata yaudara da karya

Zaka iya samun masoyi nason masoyiyarsa da gaske, amma a gaba yaji Kwata kwata baya ra ayinta. 

Haka zaka riski masoyi baya sonta amma daga karshe yaji ya fara son abunda bayaso a baya. 

A wannan Bayanin nawa zai gamsar daku cewa Bbu wanu soyayya ta Gaskiya dana karya, duk soyayya soyayyace

Cikin Mafarkina Kullum Kike Zuwa Min, Anan Nasanki. Anan Nakejin Muryanki. 

Duk Inda Kike Nasan Kina Jina Arai... 

Asonki Ba Abinda Zai Gagaran.. 

Kin Zama Abin Tunanin Garan.. 

Safiya Da Rana Harma Daran..

Nimanki Nake Ban Ganoki Ba😭

🏃

Yauda Gobe Jibi Ban Fidda Ran...

Zana Ganki Duk Dadewa Daran... 

Zana Bada Lokacina💪 Wajan Nemanki Kuma Bazanga Wahalarshi Ba


TAYA ZAKA HUKUNTA MATARKA

Duka ko zagi baya daga cikin hanyoyin da zasu bayyanawa mace kuskurenta yayin da tayiwa mijinta laifi, akwai hanyoyi masu tarin yawa wanda zaisa mace ta gane tayi maka laifi kuma da kanta zata nemi tuba awajanka

hanya mafi sauki shine janye tallafin kulawarka gareta, ba ina nufin ka daina ciyar da ita, shayar da ita ko tufatar da ita ba, kulawar danake nufi shine ka daina mata magana, hakama ko tayi maka kada ka kulata.

ku kwana tare ku tashi tare, kuci kusha duk tare amma ba magana tsakaninku. idan ta kawo maka abinci kaci, idan ta tambayeka kudin wani abu, ka daure ka bata. amma kada kace mata gashi, kawai ka ciro ka mika mata

ina mai tabbatar maka da kanta tace wane kayi hakuri bazan sake ba. anan ne saika kara mata haske akan kuskuren ko laifin da tayi maka. dan Allah maza mu daina duka ko zagin matarmu. domin su din masu rauni ne

Post a Comment

0 Comments