Header Ads Widget

Yadda Ake zama da Kishiya

 KISHIYA



Sunanta na yanka abokiyar zama , bahaushe

ne ya kakaba mata wannan suna.

Larabawa na kiranta Darratu wato cuta .

Kishita bata zama cuta sai dai wadda ta

shigo da nufin sharri.

Haka dai ake sanyawa abokiyar zama

sunaye munana wanda ya sabawa

manufarta.

Duk abinda aka kirashi kishiyar wani abu to

tabbata basu haduwa , ita ko kishiya tare

kuke a karkashin mijin daya zaune daram

watakil ma mutuwa ce zata raba.

kishiya tana zama ne tare da 'yar-uwarta ko

ita ta taras ko a iske ta .

Ko wace mace ta sani wannan zama , zama

ne na ibadah da neman yardar Allah, mai

cike da ka'idoji wanda shari'a ta shimfida

kuma ta hanyar cika su ne mace zata samu

aljannah sabanin haka kuwa zai kaita wuta

kai tsaye.

Zaman mace fiye da daya a wurin miji ba

zama ne na kiyayyaya da fitina ba kamar

yadda wasu mata suka jahilci abin.

Zama ne na yin gasa da ruge-rige wajen

neman tsira a lahira.

Zamane na taimakekeniya a tsakanin matan ,

musamman a halin rashin lafiya ko tafiya ko

ma har a bayan rayuwar daya, dayar takan

rike 'ya'yan tamkar nata ta basu tarbiyya.

Macen da ta cika mace tasan falsafar rayuwa

ta kwarai , Allah kishiya bata gabanta ! wata

ma ta kan manta tana da ita babu abinda ya

dameta dan ta riga ta samu nutsuwa ta

amshe kuma ta mallake zuciyar mijinta

wanda shine kololuwar abinda mafi yawan

mata suke kishin a kansa.

Itace matar da take ruko da addininta da

fawwala lamurranta ga Allah.

Ta sani kuma ta lakanci abinda mijinta yake

so da wanda baya so kuma take kiyayewa.

Bata da raggwanci ga himma wajen tsafa

kwalliya da iya ado.

Tana ganin girman mijinta dan haka bata

sakaci wurin yiwa mijinta cikakkiyar biyayya

, ga tsananin nuna tausayinsa , tattali da

godiya ga kokarinsa .

Sababbin kalaman Soyayya na 2023

Sakin fuskarta baya bari a san bacin ranta ,

hakurinta ya hana a gane fushinta.

Tarairayar miji kissa da kisisina hadi da

shirya haddaden abinci da iya sauke kaya a

muhallinsu , da tsaida magana a maudu'inta

yasa ta siye tunanin mijinta cikin ruwan

sanyi.

Kalaman soyayya masu sanyaya Zuciyar Masoya

Duk matar da take ganin kisiyar waje tafi ta

ciki to ta shirya sanya rigar qaya kuma ta

sani izgilanci ne ga maganar Allah.

Allah yasan hikimar da tasa yace maza su

auri mata daga biyu-biyu.

Allah ya yayewa mata kishi yabasu ikon

ganin alkhairan da yake tattare da zaman

mace fiye da daya.

Allah ya yassarewa matasa muji suna farawa

da biyu-biyu , uku-uku .

Ya ba masu mata ikon karawa hudu


MATAN DA BASU DA DADIN ZAMA 12

______________________________________

1-Matan da basu da dadin zama suna da yawa wadda tafi hadari a ciki ita ce JAHILA anan ana nufin mai karancin kula da addini koda ace karatun ta ya kai England koda taje birnin siiin tayi boko indai babu addini a tare da ita to JAHILA ce, sai ta tafka wata wautar sannan zaka gane jahilace duk karatun da tayi baya da amfani.


2-Ta biyu ita ce KAZAMA macen da bata iya kula da jikin ta ba, bata san yadda zata kiyaye tsaftar muhallin ta ba , bata san yadda zata yi kwalliya taja hankalin mijin ta ba, wannan tana da wahalar zama.


3-Mace mai bakin kishi ( kishi dabi'a ne kishi halitta ne kuma kowa yana kishi hakikani ma Maza sunfi kowa kishi Dalili mu Allah ya taya mu kishi yace kada ayi mana kishiya saboda yasan me ya ake a zukatan mu )


4-Mace mai neman ganin kwaf ( ka jawowa kanka hatsarin da bazaka iya naganin sa ba) kamar macen da zata dauki wayar mijin da tana bincike 'dawa dawa yake kira dawa dawa yake chatting' sai ta binciko ina yake zuwa wace irin mu'amala yake yi su waye abokan sa , idan wayar sa tayi ringing sai leko taga wa yake kiran sa, wannan mace itama tana da wahalar zama.


5-Mace mai jiji da kai amma a nan fa ba mai yanga ba saboda yanga siffa ce mai kyau ga mace , macen da take ganin ta fika alfarma ai aurenta ma da kayi alfarma ce aka yi maka , gidan su yafi naku ta fika kyau ta fika takardun boko da dai sauran su , to wannan mace itama tana da wahalar zama.


6-Ta shida ita ce MAKARYACIYA duk aninda akayi bata fadin gaskiya, idan mutum ya zamo makaryaci to yanada wahalar al'amari, kuma shi makaryaci ranar da yayi gaskiya ma ba za'a yarda da shi ba, to wannan mace itama tana da wahalar zama.

( PROF MANSUR SOKOTO)


MATA KU KARA NAZARI!!!

**************************

'(1). Idan Har Kika Yarda Da Cewa Namiji Ba Zai Kara Aure Ba Bayan Ya Aureki

Hakika Kin Yi Rashin Hankali 'Yan Mata, Dan Naga Wasu Har Alkawari Suke

Kullawa Da Samarin Su AKan Hakan.!


'(2). Idan Kuma Kika Ce Ba Za Ki Rike Dan Mijinki Ba (Dan Kishiya) Nan Ma Kin

Tafka Shashanci Babba, Dan Idan Kin Haifi Naki 'Ya'yan Babu Tabbacin Cewa

Zaki Dawwama a Gidan Ko A Duniyar Ma.


'(3). Idan Kuwa Kika Ce Namiji Ba Dan Goyo Ba Ne Kin Zama Sakarya,

Shashasha kuma Bagidajiya! Domin Kin Mance Da cewa"Ai Ke Ce Baki Iya

Yanda Ake Goyon Namijin Ba.


'(4). Idan Kuma Kika Ce Kishiya Ba Abokiyar Zama Bace Koh Mijinki Ba Zai karo

Wata Matar Ba Toh KeNaki 'Ya"yan Idan Kin Haifa Jere Za Kiyi Dasu Adakin ki

ne?


'(5). Idan Kika Raina Uwar Mijin Ki, Toh Ke kuma Taki Uwar Fah?

Yaya Zata Kasance Agurin Matan Yan Uwan Ki.


'(6). Idan Kika Azabtar Da Kannen Miji, Naki Kannen Fah? Yaya Za suyi Agurin

Matan Yayyinsu?


'(7). Idan Kuma Kika Ce Saurayin da Ke Nemanki Zaki Wulakanta Toh Wanda

Kike Tunanin Yana Sonki Idan Shi Kuma Ya Wulakantaki Yazakiyi?


'(8). Idan Kina Wulakanta Dangin Mijinki, Toh Naki Dangin Waye Zai Girmama

Su?


'(9). Idan Kika Ce Ke Bakya Son Kishiya Toh Sauran Yan Mata Da Zawarawan

Gari Suyi Yaya?


'(10). Idan Baki Girmama Mijinki Ba, Alamace Da Ke Nuni Da Cewa Baki Ga

Mahaifiyar Ki Tana Girmama Mahaifinki Ba.


'(11). Idan Kika Ce Ke Bakya Son Kishiya Toh Kisani, Da Yiwuwar Ayi Miki

Kishiyar Waje Wacce Idan Akayi Rashin Sa'a Kuma Kishiyar Nan Dai Taki Ta

Waje Ta Aiko Miki Da "SAKON MUTUWA" (HIV Aids)!!'SUBHANALLAH,

Dan Allah Mata A Ringa Yin Kyakyawan Tunani Da Nazari sannan Kishiya

Abokiyar Zamace saidai a yadda kika dauke ta.

Allah Yasa Mu Dace, Ameen!!!


ÆŠaurin Shekara 5 ne hukuncin wanda yayi wa Matar sa Kishiya daga Rahina law School

_______________________________________________________


Me ake nufi da Kishiya ?

Kishiya na daga cikin abubuwa masu matuÆ™ar girma da mata basa so, idan kaga an yimasu ita to ba yadda suka iya ne, domin kuwa basa son zama da ita. Duk da dai marubucin nan Tonga Abdul Tonga ya bayyana cewa ba wai zama da ita ne basa so ba, a'a su matsalar su da ita kawai shine “Haƙƙin Mallaka” ta inda za kaga wasu matan sun yarda Mijin su ya riÆ™a bin Matan banza akan yayi masu kishiya


Dan haka Baba Impossible, 2015, yake cewa: “Kishiya” ta samo asali ne daga “kishi” wanda take nufin rashin jituwa da nuna Æ™yashi irin wanda matan dake auren mutum É—aya ke yiwa juna ko kuma nuna gaba a kan wata mace. Haka kuma Kishiya na nufin abokiyar tarayya a wasu al'amuran rayuwa ta É“angaren auratayya, wato, abokiyar zama ko mataimakiyar al'amuran zamantakewar aure.


Ko Ya Halasta a dokar ƙasa a yiwa Mace Kishiya ?


Yana da kyau mu sani cewa Nigeria Æ™asa ce da ake kira da “Secular State” wato Æ™asar da babu ruwanta da addini, ko kuma Æ™asar da bata haÉ—a harkokin siyasar ta dana addini ba. Saboda haka a Nigeria muna da tsarin auratayya iri biyu ne, kamar haka:


1. Traditional Marriage:

Shine Auren da ya haÉ—a da na gargajiya ko na Musulunci, ko na wasu mabiya addini can daban, a irin waÉ—annan auratayya za kuga cewa ya halasta mutum ya auri mace daga É—aya har zuwa HuÉ—u a Musulunci kenan, idan ka koma wasu al'adun kuma za kaga ba suda iyaka wajen matan da zasu iya aura.


2. English Marriage:

Amma a English Marriage ko Court Marriage ko Civil Law Marriage, haramun ne mutum ya auri mace sama da É—aya, ko kuma ita macen ta auri namiji fiye da É—aya.

Dan haka daganan zamu fahimci cewa yiwa Mace Kishiya haramun ne a dokar ƙasa kamar yadda Sashi na 39 na Marriage Act ya bayyana.

Dan haka duk lokacin da kika ga mijin ki zai yimaki Kishiya to abinda za kiyi shine ki nemi lauyanki ku shigar da Æ™ara a babbar kotun jiha (State High Court) ko babbar kotun tarayya (Federal High Court), definitely ita kuma kotu zata dakatar dashi daga yunkurin yimaki Kishiya, idan kuma har ya riga yayi miki kishiyar to kotu zata É“ata wannan auren, kamar yadda Sashi Na 14 dana 15 ya bayyana. 


Sannan bayan kotu ta É“ata auren, zai fuskanci hukuncin É—auri a gidan Kurkuku har na tsawon Shekara Biyar, kamar yadda Sashi Na 39 Na Marriage Act ya bayyana.


NB:

Duk lokacin da kike so ki hana mijin ki yayi maki Kishiya to tun wurin yin auren kiyi masa wayau ki lallaɓa shi akan cewa kuyi English Marriage 😄 to kuna yi Shikenan kin gama dashi sai dai yaita Lahaula 😄.

Bissalam

(Shehu Rahinat Na'Allah)

5th July, 2022

Post a Comment

0 Comments