Header Ads Widget

Yadda Ake Rainon Jaririyar Soyayya

 Yadda Ake Rainon Jaririyar Soyayya



Duk wani abu mai rai daga karami yake

farawa, sannan ya girma a hankali har ya

zama gangaram!


Soyayya ma ruhi gare ta,kamar shuka ce da ake dasawa a zukata, don haka tana bukatar raino da ban ruwa, kamar dai yadda ake yi wa tsiron da aka

dasa. Idan haka ne kuwa, to ga wasu shawarwari na yadda ake rainon jaririyar soyayya.


A lura cewa akwai bambanci tsakanin

rainon jaririyar soyayya da rainon soyayya.

Zan yi bayani gaba kadan.


Ta yaya za ka yi rainon jaririyar soyayya?


Idan ya kasance akwai alkawarin wata a

kanka kuma kana da bukatar hada zumunci

na auratayya da su ko da ita ba tare da ka yi

la’akari da kyau ko sura na yarinya ba.

Ma’ana, ka aminta da duk irin halin da za ka

gan ta zuwa girmanta.


To ya kamata a ce ka bi wasu matakai don samar da wanzuwar kauna da soyayya a tsakaninku na har abada ko kuma aure. Dole ne ka tabbata

cewa tana sonka, idan ta soma mallakar

hankalin kanta. Kuma kai ne za ka sanya

mata sonka da kaunarka tun tana yarinya.

Ka guji yawan zuwa gurinta saboda zargi ko

kazafi. Ka rika share hawayenta, ba ina nufin

hawayen kuka na idanuwa ba. Ma’ana, ka

rika saya mata abin da ka ga yaro yake so ko

kuma burge shi.


Mun san cewa soyayya ba ta da tabbas, to amma yin haka shi zai sa ba za ka cire rai ga barin sauyawarta ba, idan ta mallaki hankalin kanta. Kuma daga nan ma ka ga sai ka dasa da wani sabon yanayi na dauwamar da soyayyarka a kanta. Dole ne ka guji ba ta kyauta ko kudi ba tare da

sanin iyayenta ba.


Dole ne ka rika nuna mata kauna da kulawa

a koyaushe.


Dole ne ka nuna mata muhimmancin rike alkawari saboda zamantakewarku ta dada karko. Dole ne kayi taka-tsan-tsan da irin lafazi, kalamai ko

hirar da kuke yi, musamman idan yarintarta

ta yi yawa saboda kada ta je ta rika kwashe

magana da surutu tana fada a ko’ina. Dole

ne tsarin hirarku ya canja a duk lokacin da

hankali ya soma karuwa.


Dole ne ka jure irin maganar da za ta yabo maka. Ka zama mai hakuri, sai ka ci galabar zama da ita da samun kanta a koyaushe.


Ka sani a dukkan lokacin da ka ga ta isa

mace mai hankali, to kada ka rika nuna mata

cewa an ba da kai ne gare ta ko kuma ka

rika fada mata cewa tun tana karama kake

sonta, tun lokacin ba ta iya magana ba, da

dai sauransu. Yin haka zai tarwatsa tare da

ruguza ilahirin ginin soyayyar da ka soma

tunda fari. Kuma za ka iya rasa ta har abada.

Muddin ba akwai wasa ba ne a tsakaninku.

Mafi shawara ma, kada a yi saboda wasu ba

su san wasa ba, ba kuma su iya ta ba. A duk

lokacin da ta gane tsantsar mene ne so, to

ka yi taka-tsan-tsan saboda so tsuntsu ne.

Idan ta kai ma munzalin girma, soyayyarku

da ita za ta tashi daga kan raino, yanzu

sabon lale za ka soma, kamar yanzu ka

ganta kana so; har zuwa lokacin da Allah zai

sa ka aure ta. Sai dai alakarku da ita tun tana

yarinya za ta taimaka ma ka samu kanta

cikin sauki, muddin za ka bi irin wanan

hanya to za ka yi dacen da kauna.

Post a Comment

0 Comments