Header Ads Widget

YADDA ZAKA GANE MACE TANA SONKA

 YADDA ZAKA GANE MACE TANA SONKA



𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓


wanne alamomi zangane mace tana sona tsakaninta da Allah?


𝐀𝐌𝐒𝐀👇👇🏻👇🏻


Duk da cewa dai soyayya ta gaskiya ba a gane ta a lokaci kankani kasancewar tana shiga ne sannu a hankali. Wasu sukan shiga ruɗani akan rashin ko da gaske matan da suke so da aure shin dagaske suma suna sonsu?


Gano soyayya mace na gaskiya ba wahala ne da shi ba. Saboda ita mace bata iya doguwar yaudara a soyayya. Ga wasu alamomin da zaka iya gano macen idan tana sonka da gaske


1. Da farko idan kana so ka fahimci mace na sonka sai idan kana cikin jarabawa na rashin lafiya. Duk macen da take kaunar namiji da gaske takan shiga matsainancin damuwa a lokacin da aka sanar da ita bakada lafiya👇🏻👇🏻👇🏻


         Ta hanyar sanar da ita bakada lafiya koda kuwa karya aka mata muddin ta kasa nuna damuwarta a hakan to ka tabbatar ba sonka take ba


2. A lokacin da ka shiga matsala na kuɗi a wannan lokacin ne zaka gane idan mace na sonka da gaske. Mace koda batada halin tallafamaka da kuɗi a lokacin da kake tsananin buƙatarsu👇🏻👇🏻👇🏻 


         zata nuna maka damuwarta tare da kawo wasu shawarwarin yadda za a iya samun mafita


3........ Ta hanyar abokanka da kuma ƙawayen wacce kake so zaka iya fahimtar idan mace na sonka da gaske. Ta yadda take mutunta abokanka da na kusa da kai, da irin kalamai na yabo da suke yi game da ita zaka fahimci tana sonka👇🏻


       su kuma kawayenta zaka iya jin gaskiyar yadda masoyiyar taka ta ɗaukeka daga bakunan su Yadda su ƙawayen nata suka ɗaukeka nan ma zai bayyana maka matsayinka a gunta


4........ xa ta rinka yin duk wani abu da ta san zai faranta maka rai. Mata suna nuna kulawa sosai ga wanda suka damu da shi/shine sai a yi maka abu ba tare da ka tambaya ba ko Ka nuna

kana so ba in dai an san ka damu da abin saboda son da ake maka xa a yi don a faranta maka rai Wannan duk alama ce ta ana sonka


5... Idan mace tana sonka da gaskiya babu ruwanta da wasu samarin saboda soyayya ta gaya ido rufewa yake😎💝

Post a Comment

0 Comments