Header Ads Widget

Wasikar Soyayya guda 2 zuwa ga Masoya

 WASIKAR SOYAYYA

1. Assalamranki yadade amincin allah yatabbata

agareki yake ma,abociyar kyau da kwarjini Allah

yabaki tsawon kwana mai amfani sannan inaso

nasanar dake irin soyayyar danake miki acikin

zuciyata gaskiya inasonki so Na gaskiya kuma

banida burin chutar da zuciyarki sai dai burin

bawa zuciyarki farinciki da annashuwa gaskiya

Na Dade ina begenki fiye da shikara biyu kuma

gashi zuciyata takasa jurewa shiyasa nagayawa



Tasanar dake abinda yake damuna sannan

naji duk abinda kikace amma kisani cewa inaso

kibani damar ganinki koda Na five minute domin

bayyanamiki sirrin zuciyata

Haqiqa ke kyakkyaqace ta gaban kwatance

wacce zan iya cewa babu tamkarki acikin

wannan duniya gaki fara mai dogon hanci

tamkar karas murmushinki tamkar jaririn fure

acikin furannan duniya sautin muryarki tamkar

sarewar algaita ta sarakunan duniya

Gaskiya ke kyakkyawace kinfi kowa kyau ga

dogon hanci gaki fara gaki kin iya murmushi mai

karya zuciya gaki da dinful Wanda bantaba

ganin irinsaba sai awajinki kinga kuwa dole

nabawa pic dinki muhimmanci wajin kallonsa

akowani hali domin wlh idan ina kallonsa sai naji

bani da damuwa koda ta minti daya ne🖕


2.  Assalamu Alaiki, dumbin farin ciki da annashuwa ne suke tare dani a lokacin da nake rubuta wannan wasikar zuwa gareki ya ke sanyin zuciyata, ba komai yasa hakan ba illa yadda zuciyata ta yanke shawarar aiko da kokon bara zuwa gareki don neman amincewa da yardarki ta yin soyayya tare dani, na dade ina yin shawarwari da sake-sake akan zuwa neman soyayyarki, sai yanzu ne naga hakan lallai ya dace.🌷📩


 Hakika kin zamo daban cikin mata, takunki, mu'amularki, kwalliyarki da iya maganarki duk ya sha bam-bam da na sauran mata, bana tunanin akwai wani d'a namiji da zai karanci halayenki ba tare da ya fada cikin kogin soyayyarki ba, hakanne yasa nima santsin soyayyar taki ya debeni zuwa cikin tekun kaunarki, a takaice dai ina so ki gane cewa

INA SONKI ! 💌 INA KAUNARKI !!💝

Post a Comment

0 Comments