Header Ads Widget

Labari maiban Tausayi Akan wasu masoya

 Labari mai ban tausayi akan wasu masoya 



khalifa da Saudat sun fara soyayya tun a makaranta ne inda daga baya har iyayen su suka san suna soyayya.

Khalifa da Saudat sunyi matukar shakuwa da juna sosai,domin kusan duk kowane lokaci a tare zaka gan su,ko makaranta ko a kasuwa basu yarda su rabe sai dai kwanciya da raba su.

Wasu Lokuta hatta da hutun makaranta idan aka basu,tsabar soyayyar dake tsakanin su a tare suke ida hutun makarantar.

A Soyayyar dake tsakanin Khalifa da Saudat,soyayyarSaudat tafi karfi sosai

Saudat tana matukar masifar san Khalifa aranta tamakar ace ta bashi zuciyar ta.

Aduk Lokacin da Saudat da Khalifa suka rabu makaranta bayan an tashi,ko minti 2 ba;ayi da rabuwar su Saudat zata fara turawa Khalifa da sakonnin soyayya da kalamai masu dadi.

Sai dai kuma shi Khalifa baya san wannan hali na Saudat na yawan tura masa sakonni da kira koda yaushe,harma yana ganin cewa kamar hakan takura masa take yi.

Akullum sakonnin Saudat a wayar Khalifa basu wuce wadannan kalmomi kamar haka..:


“INA SANKA”

“INA KAUNARKA”

“INA BEGENKA”

“INA KEWARKA”


Wadannan sune mafi yawan sakonnin kalaman soyayya da Saudat take yawan turowa Khalifa Kullum.

Watarana da daddare Khalifa ya kwance akan gado, sai yaji wayar sa tayi kara alamar shigowar sabon sako a wayar sa,sai dai a wannan lokacin Khalifa bai duba sakon ba,balle ko zai iya sannin waye ya turo saboda alokacin shi bacci ne kawai a gaban sa.

Khalifa ya share ya jayo bargon sa ya lulluba abun sa,ashe Saudat ce take turo masa sako shi kuma saboda da dabi’ar sa haka take bai damu ba,bayan Khalifa yayi bacci sakonnin Saudat sun cigaba da tururuwar shigowa wayar sa babu adadi har ta gaji ta daina.

Washe gari da sassafe Khalifa yana kwance ko farkawa baiyi daga bacci ba,sai can yaji an kira wayar sa,bayan Khalifa ya farka daga bacci yayi yunkura zuwa kan wayar sa don ya duba wanda ke kiran sa, ashe mahaifiyar Saudat ce take kiran Khalifa.


Bayan Khalifa amsa kiran Mahaifiyar Saudat sai yaji ta fashi da kuka,sanna

Post a Comment

0 Comments