Header Ads Widget

Zafafan kalaman Soyayya Masu Ratsa Zuciyar Masoya na 2023

 Zafafan kalaman Soyayya Masu Ratsa Zuciyar Masoya na 2023



NI NA TABBATAR DA NA YI DACE.💐


A dukkan dare zuciyata na rad'a min cewa, So ba kawai yana nufin samun abokin rayuwa bane ba, sannan kuma ba yana nufin 'kulla zazzafar soyayya a karon farko ne ba, a'a SO yana nufin samun ingantacciyar kulawa daga
wajen saurayi kyakkyawa irin ka, SO na nufin gina katangar soyayya mai 'kwarin da zata d'auki tsawon lokacin da ya kai a busa kaho adoron khasa.

Mummy tace in fidda wacce nake so na aura nan da sati biyu ko kuma amin auren dange 

RAYUWA


A lokacin da ka shigo cikin rayuwata, na ji tsoron kar ka raunata zuciyata, amma yanzu da na same ka, ina jin fargabar rasa ka. Ina fatan zuwan ranar da zan zamo mata a gare ka. 

Ina son kasancewa ne tare da wanda zai kasance cikin saka ni farin ciki, ya sa ni murmushi a lokacin da nake cikin damuwa, wanda zai kasance cikin so na a kowane irin yanayi. Na san babu wanda zai iya hakan sai kai, a saboda haka nake kara bayyana maka cewa, ina son ka. Ya Hubbina❤

Duk Soyayya tana tare da ɓacin rai amma banda soyayyar Annabi Muhammad ﷺ🌹

❤I love you with all my heart💜


Tattausan kalami zazzakar murya hadadden murmushi kayataccen kallo kyau natsuwa kunya hakuri kamala tausayi aminci allah yakara tabbata gareka malami kamili salihi hafizi haziki sarki sarkin kyawawa gami da yardah da aminci su kara kasancewa ga amintacciyar zuciya wadda so da kaunar tah suka mamaye rayuwatah hakika kai nawane domin kai kadai ne nake burin kasancewa tare dakai abin alfaharina I LOVE YOU with all my heart

Post a Comment

0 Comments